in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"Yawan ma'aikatan kwadago da suka samu ilmi a duniya ya kyautatu", in ji kungiyar ILO
2015-11-18 09:35:31 cri
Kungiyar ma'aikatan kwadago ta kasa da kasa ILO ta bayyana cewa, yawan ma'aikatan kwadago da suka samu ilmi a duniya ya karu cikin shekaru 15 da suka gabata.

Alkaluman da kungiyar ILO ta fitar, ya nuna cewa, daga cikin kasashe 64 da aka gudanar da bincike, yawan ma'aikatan kwadago da suka samu ilmi a cikin kasashe 62 ya karu cikin shekaru 15 da suka gabata. Kungiyar ta ce, akwai babban gibin tsakanin yawan mutanen da suka samu ilmi mai zurfi da yawan guraben aikin yi da ake samarwa, kuma idan ba a magance wannan matsala ba, hakan zai shafi yadda ake raya tattalin azriki nan gaba.

Bisa binciken da aka gudanar a bangaren jinsi na ma'aikatan kwadago a duniya, an ce, akwai rashin daidaito game da yawan maza da mata da suka samu ilmi a kasashe masu tasowa da kuma guraben aikin da suka samu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China