in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NBA zata yiwa yan wasa masu yawa rejista daga wajen Amurka
2016-10-26 21:05:36 cri
NBA za ta yi rejistar yan wasan kimanin 113 a kakar wasanni ta 2016-17 daga wajen kasar Amurka a yayin da ta fara gangaminta karo na 71 a ranar Talata.

Baki daya, NBA ta yiwa yan wasa da wakilai daga kasashe 41 da sauran sassa na duniya rejista. Daga cikinsu akwai 'yan wasa kimanin 61 daga kasashen turai, sai kuma yan wasa 14 daga nahiyar Afrika.

Sai dai kasar Sin ta rasa wakilci a NBA, bayan da tsohon dan wasan Dallas Mavericks, Yi Jianlian, ya nemi kungiyar wasan Los Angeles Lakers data sallameshi a ranar Litinin.

Yi, ya fada cewa, yana neman samun wata damar ne a wani wajen na dabam, sai dai akwai yiwuwar ya sake komawa kasar Sin a nan gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China