in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gabatar da shirin kasar Sin kan yadda za a yi hadin gwiwa domin tinkarar kalubaloli a yayin taron koli na BRICS
2016-10-17 10:28:28 cri

A jiya Asabar ne aka gudanar da ganawa tsakanin shugabannin kasashen BRICS karo na 8 a garin Goa na kasar Indiya, inda shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping, ya yi wani jawabi mai take "kulla imani domin neman ci gaba tare". A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya gabatar da shawarwari kan yadda kasashen BRICS za su iya tinkarar kalubaloli a cikin sabon yanayin duniya. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta yi hadin gwiwa tare da sassa daban daban, wajen tsara wani sabon shirin neman bunkasuwar kasashen BRICS.

Shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 10 da kafuwar kungiyar BRICS. A cikin shekaru 10 da suka gabata, kasashen BRICS sun ba da muhimmiyar gudummawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya. A yayin taron ganawar da aka yi, Xi Jinping ya yaba wa sakamakon da kasashen BRICS suka samu. Mr. Xi ya bayyana cewa, "Wadannan shekaru 10 ne da aka samu bunkasuwa da ci gaba tare. Mun tsaya kan matsayin mayar da kokarin neman ci gaban tattalin arziki, da kyautata rayuwar jama'a a gaban komai. Sakamakon haka, mun samu ci gaba sosai. Sannan wadannan shekaru 10 ne da muka habaka fannoni daban daban na hadin gwiwa, domin kokarin neman nasara da kuma moriyar juna. "

Har yanzu, tattalin arzikin duniya bai samu farfadowa kamar yadda ake fata ba. Ana bukatar shugabannin kasashen BRICS su kara yin hadin gwiwa domin tinkarar matsaloli tare. Sabo da haka, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarwari 5.

"Da farko dai, dole ne mu ci gaba da gyara tsarin tattalin arziki da sabunta hanyoyin neman samun ci gaba, domin kafa tsarin tattalin arziki dake iya fuskantar duniya baki daya. Na biyu, dole ne mu ci gaba da tattaunawa tsakanin kasashe masu arziki da masu tasowa, da kuma a tsakanin kasashe masu tasowa, domin samun hanyoyin bunkasa dawaumammen tattalin arzikin duniya cikin daidaito. Sannan dole ne mu yi hadin gwiwa domin tinkarar bala'u daga indallahi, da sauyin yanayin duniya, da matsalolin yaduwar annoba da ta'addanci da ake fuskanta a duk duniya, ta yadda za mu iya bayar da gudummawarmu ga kokarin tabbatar da kwanciyar hankali har abada. Bugu da kari, dole ne mu ci gaba da fadada ikon wakilci, da na ba da shawara na kasashe masu tasowa, domin kafa sabuwar dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa ta samu ci gaba tare. Daga karshe dai, dole ne mu bunkasa sabon bankin neman ci gaba na BRICS, da asusun tinkarar matsaloli cikin gaggawa kamar yadda ya kamata, domin tabbatar da bunkasa tattalin arzikin kasashe masu tasowa."

Dadin dadawa, firaministan kasar Indiya, Narendra Modi ya bayyana cewa, a sabon halin da ake ciki, ya kamata kasashen BRICS su ci gaba da yin hadin gwiwa, a fannin aiwatar da ajandar neman dawaumammen ci gaba nan da shekarar 2030, kuma su taka karin rawar gani a kungiyar kasashe 20 da ta WTO. Ya ce bangaren Indiya yana fatan kasashen BRICS za su kara gudanar da hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da zuba jari, da hada-hadar kudi da aikin gona, da aikin mayar da yankunan karkara su zama garuruwa, da samar da kayayyakin more rayuwar jama'a da dai makamantansu. Mr. Modi ya bayyana cewa, "Bayan aukuwar matsalar hada-hadar kudi a shekarar 2008, kasashen BRICS sun bayar da gudummawarsu matuka wajen tabbatar da karuwar tattalin arzikin duniya. Muna ganin cewa, ya zama wajibi ga kowane yanki ya zuba jari kan muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, da daidaita manufofin tattalin arziki domin kokarin bunkasa tattalin arziki, da kuma samar da sabon karfi ga cinikayyar da ake yi tsakanin kasa da kasa, da masana'antun samar da kayayyaki."

A waje daya, a yayin ganawar, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya shelanta cewa, kasar Sin za ta zama kasar shugabancin kungiyar BRICS a shekarar 2017, kuma za a shirya taron ganawa karo na 9 tsakanin shugabannin kasashen BRICS a birnin Xiamen na lardin Fujian, wanda ke kudu maso gabashin kasar Sin a watan Satumbar shekarar 2017.

Bayan kammala ganawa tsakanin kasashe biyar na BRICS, jagororinsu sun halarci bikin sa hannu, kan wasu takardun hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China