in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutane dake tafiye-tafiye a cikin kasar Sin a rana ta uku ta bikin kasa ya kai kimanin miliyan 108
2016-10-04 12:52:07 cri
Bisa alkaluman da hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin ta bayar, sun nuna cewa, a ranar 3 ga wata, wato rana ta uku da Sinawa suke bikin kafuwar Jamhuriyar jama'ar kasar Sin, yawan mutane dake yawon shakatawa a kasar ya kai kimanin miliyan 108, wanda ya karu da kashi 14.3 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, kana yawan kudin da aka kashe a fannin yawon shakatawa ya kai RMB biliyan 88, wato ya karu da kashi 15.1 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.

A wannan rana, masu yawon shakatawa sun fi sha'awar zuwa kauyuka da wuraren tunawa da juyin juya hali na kasar don yawon shakatawa. Yawancinsu su kan je yawon shakatawa tare da iyalai, da abokai, ko kuma su tuka mota da kansu. Bukukuwan musamman game da al'adun gargajiya da aka shirya a wurare daban daban sun jawo hankulan masu yawon shakatawa da dama. Yawon shakatawa na kallon furare, cirar 'ya'yan itatuwa, cin abinci masu dadi da dai sauransu sun kara armashin harkar yawon shakatawa a yayin wannan biki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China