Gwamnatin kasar Mali ta bayyana gamsuwarta kan hukuncin da kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa (ICC) ta yanke a ranar Talata kan Ahmad Al Faqi Al Mahdi bisa babban laifin lalata kabari da wasu dadadun wuraren tarihi da aka sanya su cikin jerin kayayyakin tarihi na UNESCO.
Hukuncin zaman kurkuku na shekaru tara ga wannan 'dan ta'adda da alkalan ICC suka yanke, wani dalili ne mai haske ga duk wadanda wannan akidar tashin hankali ta shafa da ta janyo ayyukan na 'yan ta'adda a arewacin kasar Mali, in ji gwamnatin kasar ta Mali. (Maman Ada)