in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Benin na la'akarin karfafa tsaron iyakokinta cikin shekaru biyar masu zuwa domin rage sabani da makwabtanta musammun ma Togo, Nijar, Burkina Faso da Najeriya
2016-08-25 10:54:40 cri
Bisa sabon shirin aikin na gwamnatin kasar Benin na shekarar 2016 zuwa shekarar 2021, an shirya batutuwan karfafa tsaron harabar kasa da na kan iyakoki, rage kangin talauci, da karfafa zaman rayuwar al'ummar kasar dake kan iyakokin kasar, da kuma kara huldar dangantaka tsakanin kasashen dake raba iyakokin kasa tare da ita, ta yadda za a iya amfani da hanyoyin nagari domin cigaban kasar Benin da kuma shiyya shiyya, tare da yaki da talauci.

Wata majiya ta ofishin ministan gidan na Benin, ta bayyana hakan bayan hukuncin da kotun kolin shari'a ta kasa da kasa (CIJ) ta yanke game da rikicin kan iyaka da ke tsakanin Benin da Nijar, amma kuma har yanzu kasar ta Benin na fama da matsalolin iyaka tare da makwabtanta kamar Burkina Faso, Togo, da Najeriya, duk da cewa kasar na shirin gabatar gaban kotun CIJ da wasu shaidun da ke tabbatar da iyakokin ta. Kasar Benin na raba kan iyakoki bisa tsawon kilomita 1,989 tare da kasashe makwabtanta, wanda kuma ruwa, da duwatsu suka nuna shaidar iyakar ko wace kasa, dalilin haka ne, kasar take raba iyaka bisa tsawon kilomita 306 da Burkina Faso, kilomita 266 da Nijar, da kuma raba yankin ruwa, bisa tsawon kilomita 773 da Najeriya, da kilomita 644 da Togo.(Laouali Souleymane)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China