in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci a kawo karshen rikicin bayan zabe a kasar Gabon
2016-09-05 10:39:28 cri

Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon ya nuna damuwa game da tashin hankalin da ya barke bayan zaben shugaban kasar Gabon, kana ya yi kira da'a gaggauta kawo karshen tashin hankalin a fadin kasar.

Ban, wanda a yanzu haka yake birnin Hangzhou a gabashin kasar Sin, domin halartar taron koli na kungiyar kasashe 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya G20, inda ya zanta da shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba ta wayar hannu, da kuma Jean Ping, dan takarar shugabancin kasar na Jam'iyyar DNP, ya bukace su da su kawo karshen tashin hankalin kasar.

Babban sakataren ya nuna muhimmancin amfani da hanyoyi na shari'a wajen warware duk wani rikici da ya shafi sakamakon zaben shugaban kasar.

Mai magana da yawun mista Ban ya ce, tuni ya umarci wakilin MDD na musamman dake Afrika ta Tsakiya, Abdoulaye Bathily da ya cigaba da yin aiki tare da bangarorin da abin ya shafa domin farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China