Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya ba da umurnin tura karin sojoji a yammacin kasar, inda aka fuskanci tashe tashen hankalin kabilanci bayan zabe da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 28, tare da tilastawa daruruwan mutane barin muhallinsu.
Sojojin za su kokarin maido da doka da oda a yankin tsaunuka na Rwenzori, tare da kama mutanen da ke hannu kan wadannan tashe tashen hankali a gundumomin Bundibugyo da Kasese, in ji shugaba Museveni a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
"Duk wani mai laifi zai dandana kudar wukarsa", in ji mista Museveni, tare da kara da cewa, mutanen da ke da hannu za su rayuwa tare da yin nadama kan danyen ayyukan da suka aikata.
Haka kuma, Museveni ya kira ga wadanda suka tsere da su dawo gidajensu, tare da bayyana cewa, sojoji za su tabbatar da tsaron lafiyarsu. Hukumomin wurin sun bayyana cewa, baya ga wadanda suka mutu, fiye da mutane dubu goma sun bar muhallinsu, sannan aka kone gidaje 366 tun lokacin zabukan kasar a cikin watan da ya gabata.
Tashe tashen hankali sun barke dai ne a lokacin da magoya wani 'dan takarar wurin suka bayyana cewa, mutuminsu ya fadi sakamakon magudin da aka tafka a yayin zaben kananan hukumomi. (Maman Ada)