in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun jinjina sakamakon da aka samu a gun taron koli na G20
2016-09-06 11:14:45 cri

An rufe taron koli na G20 a jiya Litinin a cibiyar nune-nune ta birnin Hangzhou na kasar Sin. An dai cimma muhimmin sakamako mai yawa, da kuma cimma matsaya daya a tsakanin kasashe daban daban a fannoni da dama a yayin taron, batutuwan da suka samu jinjinawa da amincewa sosai daga kasashen duniya. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a cikin jawabinsa a gun bikin rufe taron kolin na G20 cewa, shugabanni da manyan jami'an kasashe membobin kungiyar G20, da kungiyoyin kasa da kasa, sun yi musayar ra'ayi sosai kan ayyukan kirkiro sabbin fasahohi, da gudnaar da hadin gwiwa a fannin tattalin arziki a cikin kwanaki biyu da aka shafe ana taron na koli, domin tattaunawa kan shirin raya tattalin arzikin duniya. A karshe sun cimma matsaya daya a fannoni da dama, tare da samun wasu muhimman sakamako. Taron ya kuma samu amincewa sosai daga sassa daban daban na duniya.

A game da haka, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa,

"Taron kolin na G20 na birnin Hangzhou taro ne da ya taka rawa mai ma'ana wajen tattauna batutuwan duniya. Yadda za a raya tattalin arzikin duniya mai dorewa, da yin hadin gwiwa mai kyau a tsakanin kasa da kasa, ya zama muhimmin batun da aka tattauna sosai a gun taron. Mahalarta taron sun cimma matsaya a kan batun kirkiro sabbin fasahohi, da kayayyaki, da kuma cimma daidaito kan manufofin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa."

An bude taron koli na G20 na birnin Hangzhou ne a yayin sauyawar hanyar karuwar tattalin arzikin duniya, da kuma yin gyare-gyare kan kungiyar G20, bangarori daban daban suna sa ran taron zai lallubo bakin zaren tinkarar kalubalen tattalin arzikin duniya. Babbar direktar asusun IMF Lagarde ta bayyana cewa,

"An yi taron koli na G20 ne a yayin da ake fama da tabarbarewar tattalin arzikin duniya, da rashin samun moriya daga bunkasuwar tattalin arzikin. A gun wannan taro, an cimma matsaya daya kan batutuwa biyu, wato kara neman samun bunkasuwar tattalin arziki, da kuma yin hadin gwiwa tare da karin kasashen duniya."

Mahalarta taron kolin G20 sun tsara shirin bunkasuwar cinikayya a duniya, da kuma takardar ka'idojin zuba jari ta G20, wanda ya zama tsarin zuba jari na farko na duniya, kana za a ci gaba da goyon bayan tsarin cinikayya a tsakanin kasashe daban daban, da kuma nanata alkawarin nuna adawa da ba da kariya ga tattalin arziki. Ana sa ran tattalin arzikin duniya zai samu farfadowa ta hanyar inganta cinikayya da zuba jari a duniya. A game da haka, bayan taron ministan harkokin kudi na kasar Brazil Henrique Meirelles ya bayyana cewa, kasar Brazil da kasar Sin sun cimma matsaya daya, kan batutuwan raya tattalin arzikin duniya da zai kawo moriya ga dukkan kasashen duniya, da yin cinikayya cikin 'yanci, da kuma kara hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha. Ya jaddada cewa,

"Ina ganin cewa, cinikayya mai nagarta a duniya za ta haifar da moriya ga dukkan kasashe mambobin kungiyar G20 ciki har da kasar Brazil, hakan zai inganta karfin kera kayayyaki a kasashe daban daban. Ko da yake ana bukatar bude kofa ga kasashen waje don gudanar da cinikayya cikin gajeren lokaci, amma dole ne a kara yin la'akari, da kuma yin musayar ra'ayi domin inganta cinikayya cikin 'yanci."

Ban da tsara shirin raya tattalin arziki, an ba da sanarwar shugaba game da sauyawar yanayi a gun taron koli na G20. A game da wannan sanarwa, shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana cewa,

"A fannin tinkarar sauyin yanayi da neman samun bunkasuwa mai dorewa, an nanata alkawarin da kasashe masu ci gaba suka yi wajen tattara kudi har dalar Amurka biliyan 100 a kowace shekara, domin daidaita batun yanayi da kasashe masu tasowa ke fuskantawa."

Bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi, an cimma nasarar yin wannan taro, kuma za a ci gaba da tabbatar da sakamakon da aka samu a gun taron, domin tabbatar da neman samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai dorewa. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China