in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta fitar da takardun bashin kasa domin magance matsalar gibin kasafin kudi
2016-08-25 11:14:19 cri

Jiya Laraba kasar Sudan ta Kudi ta fitar da takardun bashin kasa domin masu zuba jarin waje za su samun damar zuba kudin a cikin ayyukansu.

Gwamnan babban bankin Sudan ta Kudu, Kornelio Koriom, ya bayyana cewa, wadannan takardun bashin kasa za su taimakawa gwamnati cike gibinsa na karancin kudi, kuma za su taimaka wajen rage hauhawar farashin kaya a kasar, da ya tashi zuwa kashi 661,3 cikin 100 a cikin watan Agusta.

Tare da bullo da wadannan takardun bashin kasa, matsin lamba game da buga sabbin takardun kudi ya bace, domin idan ana ci gaba da buga sabbin takardun kudi, haka kuma hauhawar farashin kaya tana karuwa, in ji mista Koriom a yayin bikin fitar da da wadannan takardun.

An samu kusan kashi 98 cikin 100 na kasafin kudin Sudan ta Kudu ne daga fitar da man fetur, amma samar da man fetur ya tsaya dalilin yakin basasa tun cikin watan Disamban shekarar 2013.

Mista Koriom ya bayyana cewa, Sudan ta Kudu dole ta yawaita hanyoyin samun bunkasuwarta a bangarorin da suka shafi hakar zinayi da aikin noma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China