in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsai da shirya gasar al'adun Benin na Golden Awards karo na 15 a cikin watan Satumba a Cotonou
2016-08-03 11:07:16 cri
Gasar al'adun kasar Benin na Golden Awards karo na 15, dake manufar bunkasa al'adun kasar Benin, musammun ma na rukunonin fayafai na wakokin zamani masu kyau dake mayar da hankali ga al'adun gargajiya da kuma shahararrun masu gabatar da wasanni kai tsaye, za ta gudana a ranar 3 ga watan Augusta a birnin Cotonou, a cewar kwamitin tsare tsaren wannan gasar a ranar Talata.

Gasar al'adun na da manufar bunkasa al'adun kasar Benin baki daya, a fannin kide kide, raye raye, wasannin kwaikwayo, silima da zane zane, har ma da kokarin ingiza masu fasaha kara himmatuwa wajen bullo da fasahohi na kwarai da kuma karfafa saninsu a fannonin da suka fi mayar da hankali, in ji Ali Wassi Sissy, shugaban wannan gasar al'adu. Kyaututukan da za a bayar sun hada da kyautar fitaccen faifan zamani, kyautar fitaccen faifan gargajiya, kyautar fitaccen faifan zamani bisa tunanin al'adun gargajiya, kyautar fitaccen faifan Hip-hop, Rapp, Gospel, da kuma kyautar gwanin gabatar da wasannin kai tsaye. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China