in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta bukaci wani tallafin kudi domin fuskantar matsalar fari
2016-08-20 12:39:57 cri
Babban taron Afrika kan fari, da ya gudana a Windhoek, babban birnin kasar Namibiya, ya kammala a ranar Jumma'a bayan a cimma wata sanarwar dake yin kira da neman tallafin kudin kasa da kasa ga Afrika,inda mutane miliyan 200 suke cikin barazanar karancin abinci.

Taron na tsawon mako guda ya tantance bukatu daban daban na kasashen Afrika domin rage yadda ya kamata fari da kuma bunkasa wani sahihin tsari da zai taimaka wajen kara juriya ga matsalar fari. Sanarwar Windhoek kan juriya ga fari ta samu rattaba hannun shugabannin kasashen da suka halarci taron.

Mahalartan taron sun jadadda wajabci ga Afrika na kafa wani asusun da zai kula da rage fari da kuma kafa wani kwamitin da zai kula da aiwatar da kuduran da taron ya cimma.

Shugaban Namibiya, Hage Geingob ya jaddada a ranar Alhamis da ta gabata kan muhimmancin halartar bangaren masu zaman kansu da kuma kungiyoyin fararen hula domin shiga gaban matsalar fari.

Ana bukatar dalar Amurka kimanin biliyan uku domin taimakawa kasashen da matsalar fari ta shafa dake cikin kungiyar kasashen SADC. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China