in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta lashe lambar zinare ta farko a wasan harbi a gasar Olympics ta Rio
2016-08-08 19:09:12 cri

A jiya Lahadi 7 ga wata agogon kasar Brazil ne aka shiga yini na biyu na gasar wasannin Olympics da ke gudana a birnin Rio. A gasar harbin bindiga na nisan mita 10 na mata da aka gudanar a jiya, 'yar wasan kasar Sin Zhang Mengxue ta lashe lambar zinariya bayan da ta samu maki 199.4 a karshen wasan. Wannan ita ce lambar zinariya ta farko da Sin ta samu a gasar wasannin Olympics a wannan karo..

A wannan rana kuma, 'yan wasan tsalle cikin ruwa na Sin sun burge 'yan kallo. 'Yan wasa mata biyu daga kasar Sin a wannan gasa Wu Minxia da Shi Tingmao sun sami matsayi na farko bisa maki 345.6. A sabili da haka, sun sami lambar zinariya ta biyu ta kasar Sin.

Dadin dadawa, dan wasan Sin Long Qingquan ya sami lambar zinariya a gasar daga nauyi a ajin kilogram 56 bangaren maza, inda ya yi nasarar daga kilogram 307, wanda ya karya bajinta da Halil Mutlu, dan wasan Turkiya ya kafa a duniya a gasar wasannin Olympics shekaru 16 da suka wuce.

Ya zuwa daren ranar 7 ga wata, baki daya an lashe lambobin zinariya 26 a gasar ta Olympics da ke gudana yanzu haka a birnin Rio de jenerou, a ciki, Amurka da Sin da Australia kowacensu na da lambobin zinariya uku-uku, a saboda haka suna sahun gaba a jerin kasashen dake da yawan lambobin zinariya a gasar wasannin ta Olympics.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China