A cewar jami'in, a lokacin da wani shugaba ya kama iko bisa turbar cin hanci, zai yi masa wuya sosai ya yi aiki bisa dokokin kasa a gaba. Yaki da cin hanci ta fuskar zabe a cikin kasashen yammacin Afirka, shi ne wani aiki mai muhimmanci da za a kula da shi bisa tsarin demokaradiyya na kasashen, in ji Joseph Djobenou.
Da yake magana a lokacin bude taron shekara shekara na RINLCAO, minista Djobenou, ya nuna cewa cin hanci annoba ce da ake samu ko ina, a nahiyar Afrika, har ma a dukkan kasashen duniya.
Matsalar ta zama ga al'umma da kasashe, kamar yadda ciwon kansa yake ga jikin dan adam. Duk da jajircewa da kokarin da ake yi domin kawar da shi, har yanzu yana bazuwa a cikin kasashe daban daban inda yake janyo illa sosai ga mutane, musammun ma ga masu zuba jari, in ji jami'in kasar Benin. (Maman Ada)