in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta zama kasuwa mafi girma ta motoci masu amfani da sabbin makamashi
2016-08-02 11:21:37 cri
Rahotanni game da motoci masu amfani da sabbin makamashi da hukumomin nazari suka fitar a jiya Litinin na nuna cewa, yawan motoci masu amfani da sabbin makamashi da za su shiga kasuwannin kasar Sin a shekarar 2020 zai kai miliyan 1 da dubu 450, ciki har da motoci dubu 800 da jama'a suka saya da kansu. Yanzu haka kasar Sin ta zama kasuwar motoci masu amfani da sabbin makamashi mafi girma, inda ta kera tare da sayar da motocin da yawansu ya kai dubu 497.

Rahoto game da bunkasuwar sha'anin motoci masu amfani da sabbin makamashi na kasar Sin na shekarar 2016 ya yi nuni da cewa, sakamakon sabbin manufofin da kasar Sin ta fito da su, an samu babban ci gaba a fannin nazarin fasahohin motoci masu amfani da sabbin makamashi, kuma yawan irin wadannan motoci da aka sayar ya karu sosai. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China