A kasar Afiria ta Kudu, Jaridar The Star, da ta Cape Times da sauran manyan kafofin watsa labaru sun bayar da sharhi cewa, kullum kasar Amurka tana tsoma baki cikin harkokin yankuna masu nisa, da nufin rage karfin sauran kasashe, ta hakan za ta iya tabbatar da matsayinta na mallakar duniya. Ko shakka babu a ganin Amurka, tana da ikon sarrafa kasashe daban daban a yankin tekun kudancin Sin, ta yadda za a mayar da Sin saniyar ware a yankin.
Jaridar Al-Ahram ta kasar Masar ta ba da rahoto cewa, kasar Amurka ba ta gamsu ba da matsayinta na baya bayan nan kan batun tekun kudancin Sin, a maimakon haka tana son nuna karfinta a yankin. Dalilin da ya sa ta kan aike da jiragen sama masu bincike don gudanar da ayyuka a asirce, domin sa ido kan kasar Sin.
Jaridar Perfil ta kasar Liberia ta ce, matsayin da kasar Sin ke dauka na amfani da hanyar diplomasiyya wajen warware batun tekun kudancin kasar cikin lumana, yana ta samun goyon baya daga kwararrun kasa da kasa. Jaridar ta ce, sakamakon da za a samu kan hukuncin da za a yanke game da batun tekun kudancin Sin, ba zai kawo babban tasiri ba kan yanayin da yankin ke ciki, ta kuma yi kira ga bangarori daban daban da batun ya shafa da su warware maganar ta hanyar diplomasiyya. (Bilkisu)