Dangane da wannan batu, kungiyar kula da lafiya ta MSF ta mai da martani cewa, sakamakon binciken da hukumar Pentagon ta Amurka ta fitar ya nuna cewa, rundunar sojan Amurka ba ta ba kyakkyawar kulawa ga aikin soja da ta dauka a yankin dake cike da fararen hula ba, kuma ba ta bi ainihin ka'idar yake-yake ba.
Shugabar kungiyar MSF, madam Meinie Nicolai ta ba da sanarwar cewa, ko a Afghanistan, ko a Syria, ko kuma a Yemen, bai kamata kungiyoyin dakaru su gudu daga daukar alhakinsu bisa dalili na wai ba da gangan ba su kaddamar da hare-hare kan asibiti ba.
Madam Nicolai ta sake yin kira da a kafa wani kwamiti na kasa da kasa mai zaman kansa domin yin bincike kan wannan batu.
A ranar 3 ga watan Oktoban bara ne, sojojin Amurka suka kai hari ta jiragen sama kan wata cibiyar jiyya ta kungiyar MSF dake garin Kunduz a arewacin Afghanistan, wanda ya haddasa mutuwar fararen hula 42, ciki har da jami'an kungiyar MSF su 14.