Ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar Afghanistan ta ce, an kai hari ne a birnin Lashkar Gah hedkwatar jihar Helmand. An yi musayar wuta tsakanin 'Yan sanda da dakaru masu dauke da makamai, inda dakaru masu dauke da makamai 10 suka mutu nan take, kana 'yan sanda 4 da dakaru 10 suka ji rauni.
Lardin Helmand na kasar Afghanistan wuri ne da ake noman tabar wiwi, kuma safarar tabar wiwi ta zama hanyar da kungiyar Taliban da ke wurin ke amfani da ita don samun kudin shiga. Wannan ya sa wurin ya kasance tungar dakarun kungiyar Taliban, A watan Afrilu na bana, kungiyar Taliban ta sake kai farmaki na sabon zagaye a lokacin bazara, wannan ya sa yanayin tsaro a kasar ya sake tabarbarewa.(Bako)