A jiya Lahadi a jami'ar koyon ilmin zirga-zirga ta St.Petersburg ta kasar Rasha, mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong ta halarci bikin bude cibiyar bincike ta jirgin kasa mai saurin tafiya na kasashen Sin da Rasha kuma bikin bude taron bunkasuwar jirgin kasa mai saurin tafiya na kasashen biyu.
Inda Madam Liu ta bayyana cewa, zirga-zirga muhimmin aiki ne da kasashen Sin da Rasha suke yin hadin gwiwa a kai. Kasashen biyu suna da niyya da kuma kyakkyawan tushe wajen yin hadin gwiwa a fannin bunkasa jirgin kasa mai saurin tafiya. A shekarar bara, hanyar jirgin kasa mai saurin tafiya da ta hada biranen Moscow da Kazan da kamfanonin kasashen biyu suka shimfida cikin hadin kai, ita ce hanyar jirgin kasa mai saurin tafiya ta farko ta kasar Rasha, kana ta zama daya daga cikin muhimman ayyukan shimfida hanyoyin jiragen kasa masu saurin tafiya da Sin ta kammala a kasashen waje. Ana bukatar karin fasahohin zamani da kwararru da ilmin gudanar da ciniki wajen zurfafa hadin gwiwa a fannin zirga-zirga da kuma raya tattalin arziki a cikin yanki iri bai daya. Hadin gwiwar kasashen Sin da Rasha a fannin koyar da ilmin zirga-zirga ya samu bunkasuwar da ba da taba ganinta ba a lokacin da.
Kafa cibiyar bincike ta jirgin kasa mai saurin tafiya na kasashen Sin da Rasha domin tabbatar da ra'ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka samu, ya dace da shirin raya kasa da kuma moriyar kasashen biyu cikin dogon lokaci da nan gaba. Cibiyar za ta tattara fasahohin kwararrun jami'o'i da kungiyoyin bincike da manyan kamfannonin kasashen biyu, domin bincike kan muhimman batutuwan bunkasuwar jiragen kasa masu saurin tafiya da horar da kwararru, ta yadda za a ba da tabbaci a fannin fasaha ga hadin gwiwar aikin bunkasa "hanya daya da ziri daya" da kawancen tattalin arziki na nahiyoyin Turai da Asiya.(Lami)