Kakakin ma'aikatar tsaron cikin gidan kasar Abdikamil Moalin Shukri ya bayyana cewa, dakarun tsaron kasar sun yi nasarar kwace wata mota makare da abubuwan fashewa, a lokacin da suka kaddamar da wani samamen da ya kai ga kama mayakan kungiyar guda 4 a yankin Elasha-biyaha da ke kudancin birnin Mogadishu.
Rahotanni na nuna cewa, a 'yan watannin da suka gabata sojojin Somaliya da ke samun goyon bayan dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka, sun samu nasara a yakin da suke yi da mayakan na Al-Shabaab. Koda ya ke har yanzu kungiyar tana kai hare-hare a sassan kasar daga lokaci zuwa lokaci.(Ibrahim)