in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru na kare bunkasuwar bangaren inshora a Afrika
2016-06-16 11:03:11 cri

Afrika na bukatar wata dokar da ta dace ga ayyukan inshora domin taimakawa bunkasuwar kasuwar inshora a nahiyar, in ji kwararru a albarkacin cikon shekaru 40 na dandali da babban taron AfrikaRe wato kamfanin inshorar Afrika.

Rwanda na karbar bakuncin taron AfrikaRe bisa taken "Ko Afrika tana iya jagorantar duniya? Matakai da hanyoyin warware matsaloli da suka dace domin kasancewa jagorar duniya."

Da yake magana a yayin wannan dandali da ya samu halartar kwararru kimanin 200 daga kasashen Afrika da ma sauran duniya, mista Mouley Hafid Elalamy, ministan masana'antu, kasuwanci da fasahohin zamani na kasar Morocco ya bayyana cewa, matakan siyasa na daidaita inshora da ba su da armashi sun dakile ci gaban bangaren inshora a Afrika.

Rashin bayanai da alkaluma masu sahihanci, bukatun samun jari masu inganci da aiwatar da takaitattun matakan da suka shafi yarjejeniyoyin daidaita inshora da aka gano sun kasance wani muhimmin koma baya da muhimman matsaloli ga bunkasuwar kasuwar inshorar Afrika, in ji ministan.

Kawai kashi 3,5 cikin 100 na kasuwar Afrika suke da inshora, lamarin dake bude kofar damammaki ga kamfanonin inshora a Afrika, a cewar bankin duniya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China