Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari tare da ministar kula da harkokin waje da cinikayyar kasa da kasa ta kasar Kenya Amina Mohamed, sannan kuma suka kira taron kwamitin ba da jagoranci kan hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a karon farko.
A jawabinsa Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana daukar kasar Kenya a matsayin kasar da Sin za ta gudanar da gwajin hadin gwiwa da ita a fannin raya karfin kera kayayyaki. Kasar Sin tana son hada kai tare da kasar Kenya wajen aiwatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika da ya gudana a birnin Johannesburg, domin inganta huldar dake tsakanin kasashen biyu.(Lami)