in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi allawadai da harin ta'addanci a Istanbul
2016-06-08 10:01:35 cri

Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya yi allawadai a ranar Talata da harin ta'addancin da aka kai birnin Istanbul na kasar Turkiya, wanda ya halaka mutane goma sha daya. Ya bayyana fatansa na ganin an gano masu hannu kan wannan hari tare da gurfanar da su gaban kuliya.

Shugaban MDD ya isa da ta'aziyya ga iyalan mamatan, tare da kuma fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata, in ji kakakin MDD Stephane Dujarric a yayin wani taron manema labarai. MDD na goyon bayan al'umma da gwamnatin Turkiya a wannan mawuyacin lokaci, in ji jami'in.

Fashewar ta faru a ranar Talata da safe a tsakiyar Istanbul, wacce aka zaton wata mota makare da boma bomai ta janyo a lokacin wucewar wata motar 'yan sanda, lamarin da ya hadasa mutuwar mutane goma sha daya, tare da jikkata wasu gomai. Daga cikin wadanda sukamutu, akwai jami'an 'yan sanda bakwai, cewar kafofin kasar.

Harin ya faru da misalin karfe 8 da minti 15 na safe bisa agogon wurin, a wurin dake da cinkoson jama'a. Inda motar makare da boma bamai ta fashe a lokacin wucewar wata motar 'yan sanda a Vezneclier, unguwar dake samun tururuwar 'yan yawon bude ido dake birnin Istanbul. Har yanzu dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China