in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Burundi ta nuna matukar adawa da takunkumin EU
2016-03-16 10:08:40 cri

Gwamnatin kasar Burundi ta nuna matukar rashin jin dadin ta, game da matakin da kungiyar tarayyar Turai ta EU ta dauka a baya bayan nan, na hana kasar damar samun tallafi kai tsaye daga kungiyar.

Wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar, ta rawaito kakakin gwamnatin Burundin Philippe Nzobonariba, na cewa EU ba ta yi la'akari da muhimmin ci gaban da aka samu a fannin tsaron kasar ba, duk kuwa da barazanar ta'addanci daga kungiyoyin masu tada kayar baya dake farwa fararen hula da aka fuskanta a baya.

Nzobonariba, ya ce, tuni kasar ta shawo kan matsalar tsaro, sai da kuma mai yiwuwa ne matakin da EUn ta dauka ya sake karfafa gwiwar masu tada kayar bayan, wadanda ka iya daukar wannan mataki a matsayin nasarar ta'asar da suke aikatawa.

A daya bangaren kuwa, jakadan EU a Burundi Patrick Spirlet, ya bayyana cewa, kungiyar na iya sauya matsayar ta, muddin Burundi ta amince ta gudanar da sauye-sauye a fannin siyasa da kare hakkokin bil'adama.

Burundi dai na fuskantar kalubale ta fuskar siyasa, tun daga watan Afirilun shekarar bara, lokacin da shugaban ta Pierre Nkurunziza ya ayyana bukatar yin tazarce a karo na uku, matakin da bai yiwa 'yan adawar kasar dadi ba. Tuni dai rikicin da ya biyo bayan hakan ya haifar da salwantar rayukan 'yan kasar sama da 400.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China