Za dai a gudanar da taron (S&ED) na tattalin arziki, da na (CPE) wanda ya shafi musaya tsakanin al'ummun kasashen biyu ne a nan birnin Beijing, a ranekun 6 da 7 ga watan Yuni mai zuwa.
Ana dai sa ran mataimakin firaministan kasar Sin Wang Yang, da dan majalissar zartaswar Sin Yang Jiechi ne za su jagoranci taron da ya jibanci tattalin arziki, yayin da kuma mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong da sakataren wajen Amurka John Kerry za su jagoranci taron musaya tsakanin kasashen biyu. Harkar musaya tsakanin sassan biyu dai ta kunshi fannin ilimi, da na kimiyya da fasaha, da raya al'adu, da kiwon lafiya. Sauran sun hada da inganta harkar wasanni, da bunkasa rayuwar mata da matasa.
Da yake tsokaci game da gudanar da tarukan, Mr. Lu ya bayyana cewa Sin na da nufin aiwatar da manufofin da ke karkashin yarjeniyoyin da ta cimma da Amurka, don haka ya dace sassan biyu su ci gaba da bunkasa hadin gwiwa tare da warware banbance banbancen dake tsakaninsu. Kana su kara azama wajen gina sabon tushen ma'amala tsakanin su. (Saminu Hassan)