in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka sun kammala shirya takardun yarjejeniyar inganta harkokin zuba jari
2015-03-07 16:09:52 cri
Kasashen Sin da Amurka sun kammala shirya wasu takardu, na yarjejeniyar inganta harkokin zuba jari da aka yiwa lakabi da BIT.

A cewar ministan ma'aikatar cinikayyar kasar Sin Gao Hucheng, duk da banbancin matsayin tattalin arziki dake tsakanin kasashen biyu, da kuma banbance-banbance a fannin manufofi, musayar da suke ci gaba da aiwatarwa za ta taimaka matuka, wajen magance kalubalolin da ake fuskanta ta fuskar cinikayya da harkokin zuba jari.

Mr Gao wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Asabar din nan, ya kara da cewa musayar takardun da bangarorin biyu ke yi, na taimakawa wajen gano matsalolin dake zama tarnaki ga masu zuba jari a kasashen biyu. Matakin da a cewarsa za a ci gaba da aiwatar da shi a nan gaba.

Game da daukar makamancin wannan mataki tsakanin Sin da kasashen Turai kuwa, Mr. Gao ya ce kasarsa ta karbi takardun bayanai karkashin tsarin na BIT, bisa umarnin sabbin jagororin kungiyar tarayyar Turai ta EU.

Ya ce Sin za ta nazarci wadannan takardu, kafin daga bisani ta gabatar da nata ra'ayi, don gane da matsayarta bisa manufofin da EUn ta gabatar mata. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China