A cewar rahoton, wadannan kasashe uku, za su iya gogayya da Afirka ta Kudu wajen neman matsayin farko a fannin kirar motoci a nahiyar Afirka. Yanzu haka dai Najeriya na amfani da sabon shirin sa kaimi ga saka jari, don jawo jarin waje a fannin sana'o'in kirkire-kirkire a kasar.
A daya bangaren kuma, cikin 'yan shekarun nan ita ma kasar Kenya ta fara kera motoci. Yayin da kasar Habasha ita ma, duk da cewa ba ta dauki wani mataki na daban a fannin kirar motoci ba, yawan al'ummar ta, da kuma makoma mai haske da take da su wajen raya kasuwar kera motoci ya sa tana iya cimma babbar nasara a fannin.
Kididdiga dai ta nuna cewa, yanzu yawan mutanen da ke da motoci a nahiyar Afirka ya kai kashi 4.4 cikin 100, adadin da ya kai kaso 18 cikin 100 a duniya baki daya. A shekarar ta 2015, an sayar da sabbin motoci da yawan su ya kai miliyan 90 a duniya, cikin adadin, miliyan 1.55 kawai al'ummun nahiyar Afirka ne suka mallake su.(Bako)