Kungiyar agaji da Red Cross ta kasar Kenya (KRCS) ta bayyana cewa, an kara gano wasu mutane uku da ke da sauran numfashi kwanaki shida bayan ginin nan mai hawa 6 da ya rufta a birnin Nairobin kasar Kenya sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sheka.
Kungiyar ta Red Cross ta ce, mutanen uku suna cikin koshin lafiya, kuma tuni aka garzayar da su asibitin Kenyatta domin a kara duba lafiyarsu, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto da fatan gano karin mutanen dake da sauran ganin badi karkashin ginin da ya rufta a daren ranar Jumma'ar da ta gabata.
Kakakin kungiyar Anthony Mwangi ya ce, ana taka-tsan-tsan wajen gudanar da aikin ceton, saboda ana sa ran kara gano wasu mutanen da ransu.
Ya zuwa yanzu dai, mutane 36 ne suka rasu yayin da sama da mazauna ginin guda 70 suka bace, baya ga mutane 140 da aka gano.(Ibrahim)