Kwamishinan Gundumar Manhera, Frederick Shisia yace wadansu kungiyoyi masu zaman kan su tuni suka fara janye wassu ma'aikatan su domin tsoron wannan hari da kungiyar masu tsatsauran ra'ayin addini ke yi dalilin sakonnin nuna kiyayya da ake ta bazawa ta kafofin sada zumunta.
Yace kungiyoyi masu zaman kansu suna janye ma'aikata daga kananan gundumomin Banisa, Takaba da Mandera ta gabas.
Mr. Shisia a hirar shi da manema labarai a gundumar Manderan yayi bayanin cewa mayakan al-shabaab wadanda a watan jiya suka hallaka sojojin kasar Kenya da dama a lokacin harin a kudancin Somaliya, suna cigaba da canza salo, yana mai lura da cewa sakonni na da nufin saka tsoro ne a zukatan jama'a da kuma korar kungiyoyi masu zaman kansu.
Ya tabbatar da cewar an lura'yan kungiyar sun canza salon a dabarun kai harin su. Don haka salon jami'an tsaron shi ma ya canza domin a tunkare su gaba da gaba.
Kwamishinan gundumar har ila yau yace jami'an tsaro dake kula da muhimman wurare da suka hada da Fino,Jillo, Dabacity, Lafey da kuma Arabiya sun riga sun mamaye ko ina tare da dawo da tsaron su.