Bankin duniya ya ce, ya ware bashin dalar Amurka biliyan 10, domin tallafawa ayyuka dabam-dabam na inganta jin dadin rayuwa jama'ar kasashen Afrika tare da bunkasa tattalin arzikinsu.
Mataimakin shugaban bankin duniya Makhtar Diop shi ne ya bayyana hakan a Maputo, a lokacin wani taron kwanaki biyu na farfado da Afrika, wanda gwamnatin Mozambique da asusun bayar da lamuni na duniya IMF suka shirya.
A yayin da take jawabi a kan taron, Diop ya ce, akwai matakai dabam dabam da suka wajaba da za'a dauka domin kawo sauyi a Afrika a kokarin da ake yi na bunkasa habbakar tattalin arziki a nahiyar.
Darektan asusun IMF Christine Lagarde ta gana a ranar Alhamis da ministocin harkokin kudi da kuma shugabannin bankunan kasashen Afrika, wadanda dukanin su sun halarci taron.
Lagarde ta ce, hasashe na nuni da cewar, za'a sami haske a kokarin da ake yi na bunksa tattalin arzikin nahiyar ta Afrika. (Suwaiba)