in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bunkasa harkokin cinikayya tsakanin kasashen Afirka ita ce hanyar farfado da masana'antun nahiyar, in ji Bankin Afrexim
2016-05-04 10:04:21 cri

Shugaban bankin shige da fice na Afirka wato Afrexim, Benedict Oramah ya bayyana cewa, muddin aka bunkasa harkar cinikayya tsakanin kasashen da ke nahiyar, ko shakka babu hakan zai kai ga bunkasa masana'antun nahiyar, ta yadda za su yi tasiri a duniya.

Shugaban bankin wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a taron harkokin cinikayya da tsarin biyan kudi da kuma tasirinsa ga nasarar bunkasa cinikayya tsakanin kasashen Afirka, ya ce, halin da nahiyar ta tsinci kan a ciki na kasancewa kurar baya a bangaren ci gaba, ya faru ne sakamakon yadda al'amura suka tabarbare a nahiyar baki daya.

Jami'in ya ce, duk da cewa, Allah ya albarkacin nahiyar da kasashe 54 a cikinta, amma nahiyar ce ta baya a bangaren kayayyakin more rayuwa, da hadin gwiwar bankuna, sannan uwa uba ta baya a bangaren cinikayya tsakanin kasashenta.

A nata jawabin, kwamishinar kungiyar tarayyar Afirka mai kula da harkokin cinikayya da masana'antu, Fatima Haram Acyl ta bayyana cewa, muddin ana son a bunkasa harkokin cinikayya tsakanin kasashen da ke Afirka, wajibi ne a bullo da harkokin kasuwanci da kuma guraben ayyukan yi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China