in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jarin da Sinawa ke zubawa a Afirka yana kara inganta makomar kasuwannin nahiyar
2016-03-11 09:58:22 cri

Masana a harkar rukunin gidaje sun bayyana cewa, yadda Sinawa ke zuba jari a wannan bangare a nahiyar Afirka ya yi tasiri a bangaren kadarorin kasar.

Shugaban tuntuba kan harkar rukunin gidaje na Knight Frank da ke kasar Kenya, Peter Welborn wanda ya bayyana hakan yayin zantarwarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin a birnin Nairobin kasar Kenya, ya ce, yanzu haka ana fuskantar karancin ofisoshin haya a wasu kasashen Afirka, kamar Tanzaniya, sakamakon yadda Sinawa ke gina gidaje da shaguna a sassan kasar.

Welborn ya ce, yadda Sinawa ke zuba jari a kasashen Afirka ya taimaka wajen rage kudaden haya, matakin da masanin ya ce, zai inganta makomar nahiyar.

A cewarsa, yanzu haka galibin Sinawan da ke aikin samar da kayayyakin more rayuwa a kasashen Afirka, za su fara karkata ga bangaren gina rukunin gidaje. Sannan akwai kyakkyawar fahimta tsakanin mazauna wadannan yankuna da Sinawa da ke harkar zuba jari a bangaren gina rukunin gidajen.

Shi ma babban darektan kamfanin na Knight Frank Kenya, Ben Woodhams ya bayyana cewa, yanzu haka Sinawa da ke harkar zuba jari sun fara taka muhimmiyar rawa a bangaren rukunin gidajen na kasar Kenya, lamarin da ya tilastawa 'yan kwangila na cikin gida rage ribar da za su rika samu.

Bayanai na nuna cewa, farashin gidaje zai kara raguwa, sannan masu sana'ar zuba jari a bangaren kadarori za su kara samun riba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China