A ran 18 ga wata, zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD Mista Liu Jieyi ya yi kira ga kasashen duniya da su ba da taimako ga kasashen da ke yammacin Afirka da yankin Sahel, don yaki da laifuffukan da ake aikatawa a tsakanin kasa da kasa ciki har da fataucin miyagun kwayoyi. Liu ya ce, ya kamata MDD ta kara amfaninta na sulhuntawa, da daidaita rarraba albarkatu, ta yadda za a iya ba da tabbaci ga kokarin da kasashen da kungiyoyin da abin ya shafa suke gudanarwa.
A gun taron tattauna matsalar fataucin miyagun kwayoyi a yammacin Afirka da yankin Sahel da aka yi a wannan ranan, Mista Liu Jieyi ya yi nuni da cewa, laifuffukan fataucin miyagun kwayoyi da ake yi kuma ake mayar da yammacin Afirka da yankin Sahel a matsayin mahadansu suna kawo babbar illa ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma a yankin, tare da kawo barazana ga zaman lafiya da zaman karko a yankin.
A sa'i daya kuma in ji shi, kasashen da ke yankin suna fuskantar kalubaloli kamar karancin albartaku da fasaha da kwarewa yayin da suke fama da fataucin miyagun kwayoyi, sabo da haka ne suke bukatar taimako daga kasashen waje cikin gaggawa.
A gun taron kuma, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wata sanarwar shugaba, inda aka yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su dauki matakai a fannoni daban daban don yaki da laifuffuka da wasu kungiyoyin duniya suka aikata a tsakanin kasa da kasa a yammacin Afirka da yankin Sahel. Sanarwar ta jaddada cewa, wajibi ne a inganta hadin kai a tsakanin shiyya-shiyya da kasashen duniya kuma a bi hanyoyi daban daban cikin daidaici, domin warware matsalar fataucin miyagun kwayoyi da kuma yaki da sauran laifuffukan da makamancin haka.(Danladi)