in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya bukaci cikakken biyayye da yin tsayin daka daga hukumomin tsaro
2015-05-19 20:51:23 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada tsayuwa tsayin daka da cikakken biyayye ga jam'iyyar a lokacin duk wani kalubale domin kiyaye tsaron kasa da daidaiton al'umma.

Shuyga Xi wanda ya bayyana hakan a ranar Talatan nan lokacin taron da ya yi da wassu manyan hukumomin tsaron kasar, yace tun da ana fuskantar sauyi masu sarkakkiya da kuma sauri a gida da waje da babban rashin tabbas da kuma hadari, hukumomin tsaro ya kamata su kara karfafa matakan kare kasa da samar da daidaiton al'umma.

Yace shugabancin tsakiya ya dora babban muhimmanci akan tsaron kasa kuma kasar zata inganta matakai na hana tare da dakile duk wani aikin da zai zama akasin haka.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China