A safiyar wannan rana da misalin karfe 7, rukunin 'yan sandan kiyaye zaman lafiya na 4 na Sin ya karbi aiki daga hannun rukunin 'yan sandan Jordan a babbar kofar ma'aikatar harkokin waje ta Liberiya.
Tun shekarar 2015 zuwa yanzu, tawagar musamman kan batun Liberiya ta MDD ta rage rundunonin sojojin kiyaye zaman lafiya na kasashe da dama a Liberiya. Rukunin 'yan sanda ta 4 ta Sin ta sauya wuri daga birnin Greenville dake kudu maso gabashin kasar zuwa birnin Monrovia, hedkwatar kasar. A sabili da haka, ta zama rundunar daya tak dake tabbatar da zaman lafiya a hedkwatar kasar, wadda ke daukar nauyin ba da kariya ga babban ginin ma'aikatar harkokin waje. Idan an kai hari ko yin barazana a kai, dole ne kungiyar ta ba da agaji ga hukumomi masu tabbatar da tsaro cikin lokaci.(Fatima)