in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EAC ta nada sabon jami'i mai shiga tsakani kan rikicin Burundi
2016-03-03 10:06:27 cri

Kungiyar tarayyar kasashen gabashin Afrika EAC ta nada tsohon shugaban kasar Tanzaniya Benjamin Mkapa a matsayin jami'i mai shiga tsakanin bangarorin da ba sa ga maciji da juna don tattaunawar sulhu game da rikicin siyasar kasar Burundi.

Shugabannin na EAC, sun sanar da wannan mataki ne bayan kammala taron shiyya da suka gudanar a birnin Arusha na kasar Tanzaniya.

A cewar shugaban EAC John Magufuli, tsohon shugaban Tanzaniyan zai gudanar da aikin sa ne karkashin jagorancin shugaban kasar Uganda Yoweri Kaguta Museveni.

Ya kara da cewar, shugabannin kasashen sun dauki wannan mataki ne domin ganin an kawo karshen rikicin na Burundi cikin hanzari.

Shi dai Mkapa, ya shahara wajen iya warware rikicin siyasar kasashen dake shiyyar, kuma shi ne mutumin da ya jagoranci shiga tsakanin don warware rikicin siyasar kasar Kenya a lokacin da al'amurra suka rincabe bayan barkewar rikicin bayan zabe a kasar a shekarar 2007.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China