in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kasance a kan gaba wajen fitar da kayayyakin al'adu a duniya
2016-03-11 10:07:07 cri

Kasar Sin ta kasance a kan gaba a duniya wajen fitar da kayayyakin al'adu zuwa kasashen ketare a shekarar 2013, inda ta zarce kasar Amurka.

Hukumar kula da harkokin ilimi, kimiyya da al'adu ta MDD, wato UNESCO ce ta bayyana hakan cikin rahoton da ta fitar a jiya Alhamis. Sabon rahoton hukumar ya nuna cewa, darajar yawan kayayyakin al'adun da kasar Sin ta fiyar zuwa kasashen waje ya kai dala biliyan 60.1, adadin da ya ninka wanda kasar Amurka ta fitar na dala biliyan 27.9.

Darektar cibiyar kididdiga ta UNESCO Silvia Montoya, ta bayyana cewa, wannan alama ce da ke nuna yadda kamfanonin al'adu ke taka rawa a harkokin tattalin arziki na duniya, inda manyan kasashe ke ci gaba da jagorantar harkar fitar da kayayyakin al'adu.

Rahoton cibiyar ya nuna cewa, kayayyakln hannu na daga cikin kayayyakin al'adu da ke matakin 10 na farko da aka yi cinikayyar su wadda darajar su ta kai dala biliyan 19 a shekarar 2013.

Sai dai rahoton cibiyar ya bayyana cewa, cinikin kayayyakin fina-finai ya ragu da kashi 88 cikin 100 daga shekara 2004 zuwa shekara 2013, yayin da cinikayyar kayayyakin kide-kide shi ma ya fuskanci koma baya a wadannan shekaru.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China