in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakiliyar UNESCO ta yi kira ga zaman lafiya a Burundi
2016-01-14 10:35:51 cri

Madam Beate Klarsfeld, manzon musammun ta hukumar UNESCO, ta kai ziyara a kasar Burundi a ranar Litinin domin iyar da sakon zaman lafiya, shawarwari da sassanta juna, a cewar wani labari mai tushe daga UNESCO.

Madam Klesfeld za ta gana a tsawon mako da shugabannin siyasa da wakalan kungiyoyin fararen hula, musammmun ma matasa. A cikin sanarwarta, madam Klersfel ta bayyana cewa, "Zan je Burundi, inda al'ummomin kasar suka jima suka fuskantar wahalhalun yakin basasa, domin isar da sakon nuna damuwa da girmama rayuwar dan adam."

Rikicin siyasar da Burundi ke fuskanta zai iya haifar da wani bala'in jin kai. Kashe kashen mutanen da aka yi a shekarar 2015 na nuna alamu na tashin hankali mafi muni. Tattaunawar da aka fara tsakanin dukkan bangarori, a karkashin jagorancin kungiyar tarayyar Afrika, MDD, kungiyar tarayyar Turai da dukkan abokan ba da tallafin ci gaba na Burundi, ita ce hanya guda da za ta iya maido da zaman lafiya da zaman jituwa tsakanin dukkan al'ummomin wannan kasa, in ji wannan jami'ar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China