in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudin da ake kashewa a fannin bincike da ci gaba a Sin na matsayi na biyu a duniya, in ji UNESCO
2015-11-11 10:17:14 cri

Yawan kudaden da ake kashewa a fannin bincike da ci gaba (R&D) a kasar Sin ya kwashe a halin yanzu kashi 20 cikin 100 bisa na adadin duniya, a gaban tarayyar Turai (EU) da Japan, tare da rike matsayi na biyu a duniya, bayan kasar Amurka, a cewar wani rahoton baya bayan nan na UNESCO kan kimiyya da aka gabatar a ranar Talata a cibiyar dake birnin Paris a yayin bikin ranar duniya ta kimiyya.

Wannan rahoto mai taken "Rahoton UNESCO kan kimiyya, zuwa shekarar 2030" na nuna cewa, kudaden da ake kashewa R&D a duniya sun ci gaba da karuwa a tsawon shekarun baya bayan nan, kuma yawancin kasashe, duk matsayinsu na kudaden shigarsu, na dora muhimmanci sosai kan bincike da kirkire kirkire domin bunkasa tattalin arzikinsu cikin karko da kuma ingiza bunkasuwarsu.

A cewar rahoton, duk da rikicin tattalin arzikin shekarar 2008 da ya shafi tattalin arzikin kasashe masu ci gaban masana'antu, kudaden da ake kashewa tsagoransu na R&D a duniya sun karu da kashi 31 cikin 100 tsakanin shekarar 2007 da shekarar 2013, wanda ya cimma dalar Amurka biliyan 1478 a shekarar 2013, bisa ga na shekarar 2007 dake dalar Amurka biliyan 1132, abin da ya karu cikin sauri fiye da GDP a duniya bisa lokaci guda da kashi 20 cikin 100.

A halin yanzu, kasar Amurka ce ta farko da kashi 28 cikin 100 na R&D, sannan kasar Sin da kashi 20 cikin 100, tarayyar EU kashi 19 cikin 100, kana kasar Japan kashi 10 cikin 100, a yayin da kashi 23 na R&D ya fito daga sauran kasashen duniya dake shafar kashi 67 cikin 100 na al'ummar duniya, a cewar wannan rahoto, tare da kara bayyana cewa, kokarin da kasashen Brazil, Indiya da Turkiya suka yi ya karu cikin sauri. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China