in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar EAC ta kaddamar da shirin raya masana'antun kasar
2015-04-10 14:21:14 cri

Bisa labarain da kafofin watsa labaru na kasashen Afrika suka bayar, an ce, a kwanan baya, ofishin sakataren kungiyar hadin gwiwar kasashen gabashin Afrika EAC da kungiyar raya masana'antu na M.D.D. wato UNIDO sun kaddamar da wani shirin raya masana'antun kasashen kungiyar EAC.

Kungiyar UNIDO za ta taimakawa kasashe 5 na kungiyar EAC don tsara manufofin raya masana'antun cikin gida na kasashensu da kuma aiwatar da su. Ko wace kasa ta kungiyar na da nata albarkatun ma'adinai, kuma za a manna takarda kan duk kayayyakin daga wadannan kasashe da bayanin kera su a EAC don fitar da su zuwa kasashen waje tare. Wannan mataki da aka dauka ya kasance wani muhimmin aiki cikin shirin raya masana'antu daga shekarar 2012 zuwa shekarar 2032 da aka zartas da shi a gun taron kolin kungiyar da aka yi a Bujumbura na kasar Burundi.

Babbar ka'idar da aka bi wajen tsara manufar raya masana'antun kungiyar EAC ita ce, a gabatar da manyan fannoni da ya kamata a raya su a farko, sannan a kafa sassan masana'antun dake hadin gwiwa da kasashen duniya baki daya, don sa kaimi ga kungiyar da ta kammala aikin raya masana'antu kafin shekarar 2032. Bisa shirin da aka yi, daga shekarar 2012 zuwa shekarar 2017, kungiyar za ta kammala aiki na farko, don sa kaimi ga raya masana'antunsu da kansu, da kuma samun bunkasuwa cikin daidaito.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China