in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNDP na bikin cika shekaru 50 da kafuwa
2016-02-25 10:30:24 cri

Shirin raya ci gaban kasashe na MDD wato UNDP, wanda ya kasance a matsayin shirin yaki da talauci mafi girma a duniya, yana gudanar da ayyukansa a kasashen duniya sama da 170, kuma a Larabar da ta gabata ne aka gudanar da babban taron kungiyar domin murnar cika shekaru 50 da kafuwar shirin a birnin New York.

Shirin dai ya yi fice ne a duniya musamman wajen ba da fifiko ga fannin ci gaban ilmi da samar da daidaito tsakanin jinsi ta hanyar yin hadin gwiwa da gwamnatocin kasashen duniya, kuma shirin ya yi aiki ne tare da wasu kasashen duniya mafiya talauci domin inganta yanayin rayuwar jama'ar kasashen, da samar da daidaito, da shawo kan matsalar sauyin yanayi da inganta harkar noma da kamun kifi da kuma bunkasa ci gaban fannin ilmi da kiwon lafiya.

Sama da ministocin kasashen duniya 80 ne suka isa birnin New York domin halarci taron bikin murnar cika shekaru 50 da kafuwar hukumar. An dai shafe wunin wannan rana ana yin bita game da irin nasarorin da shirin ya cimma cikin shekaru 50, sannan daga bisani aka sake yin nazari game da sabbin matakai da za'a dauka a wasu shekarun 50 masu zuwa, kuma za'a fara aiki ne kan muradu 17 na ci gaba wanda ake sa ran cimma su nan da shekara ta 2030.

Shirin UNDP, ya kasance a kasar Sin sama da shekaru 30 da suka shude, kuma kasar Sin ta cimma gagarumar nasara wajen aiwatar da wannan shiri a tsawon lokaci.

Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya fada cewar, har yanzu kasar Sin tana da burin ci gaba da inganta rayuwar Sinawa wajen cire su daga kangin talauci a cikin shekaru masu zuwa.

Liu, ya kara da cewar, cikin shekaru 5 masu zuwa kasar Sin tana bukatar cire mutanen kasar miliyan 70 daga cikin kangin talauci, karkashin shirin kasar na yaki da talauci, kuma wannan ya gwada cewar, cikin kowane wata, mutane miliyan guda ne ake tsamewa daga cikin kangin fatara.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China