Yayin da aka tabo maganar iyalinsa, Liu Gaoqiong yana farin ciki sosai. Kafin gudanar da bikin sabuwar shekarar gargajiya ta Sinawa, ya dauki matarsa da yaransa don koma garinsa na asali dake lardin HuNan.
Liu Gaoqiong ya gaya wa wakilinmu cewa, yaransa suna son jirgin kasa mafi sauri da ke kasar Sin, kuma suna mamaki, sun dauki hotuna da dama.
Nan da wasu shekaru kadan, Liu Gaoqiong zai yi ritaya, kuma Liu Gaoqiong yana fatan ci gaba da aiki a jami'ar Egerton don ba da gudummawa ga aikin gona a kasar Kenya.
Don sa kaimi ga raya aikin gona a kasar ta Kenya, Sin ta tura kwararru a fannin aikin gona da dama zuwa kasar Kenya kamar su Liu Gaoqiong, ban da wannan kuma, Sin ta kafa cibiyar taimakawa kasashen Afrika game da aikin gona, kana kuma ta shirya kwararru a fannin aikin gona na kasashen Afrika don su yi karatu a kasar Sin, abun da ya sa kaimi ga raya aikin gona a nahiyar.(Bako)