A bisa irin kokarinsa, yanzu yawan tumatir da aka samu a dakin dumi ya kai Ton dubu 10 a ko wace ekka, wanda ya karu sosai bisa lokacin baya.
A shekarar 1998, shugaban kasar Kenya na wancan lokaci Daniel Arap Moi, ya ziyarci jami'ar don halartar bikin da aka yi a wurin, kuma ya gane ma idanunsa shuke-shuken tumatir a dakin dumi da Liu Gaoqiong ya yi.
Bayan da ya gano yadda tumatir da Mr. Liu ya shuka ya yi kyau, shugaban Moi ya yi farin ciki da cewa, da za'a iya samun yawan tumatir a sauran wurare kamar yadda aka samu a dakin dumi, jama'ar kasar Kenya ba za su gamu da yunwa ba.
Yanzu haka a wasu wuraren na kasar Kenya zaka ga mutane suna shuka tumatir a dakin dumi, kuma hakan nada alaka ne da irin gudummawar da Liu Gaoqiong ya bayar.
Don ci gaba da bunkasa aikin gona a kasar Kenya, yanzu haka jami'ar koyon fasahar aikin gona ta birnin Nanjing ta kafa dakin gwajin halittu a jami'ar Egerton. Ban da aikin koyarwa na yau da kullum, a ko wace rana Liu Gaoqiong ya kan taimakawa bangaren kasar Kenya don fahimtar yadda aka sarrafa na'urorin dake cikin dakin gwajin, don gudanar da nazari.
Yanzu, ba ma kawai Liu Gaoqiong ya gudanar da aikin gona a kasar Kenya ba, har ma ya kafa iyali a wurin, ya yi aure da wata 'yar kasar Kenya, kuma yanzu ya haifi yara 3.