in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararre a fannin aikin gona ya yi zama a kasashen Afrika na tsawon shekaru 20 don taimakawa aikin gona a yankunan
2016-02-25 13:50:55 cri


A jami'ar Egerton da ke kasar Kenya, yayin da aka tabo maganar Kwararre a fannin aikin gona na kasar Sin Liu Gaoqiong, kowa zai jinjina masa game da babbar gudummawar da ya bayar a fannin aikin gona a kasar Kenya.

Liu Gaoqiong ba ya da tsayi sosai, kuma yana da bakar fata, duk da cewa shekarunsa sun kai 50 da wani abu kawai, amma gashin kansa ya yi fari sosai. Yayin da aka tabo maganar fasahar aikin gona, sai ya fara tofa albarkacin baki, don nuna kaunarsa game da aikin gona, kuma ya tashi tsaye don nazarin aikin gona, har ya kai ziyarar aiki a kasar Kenya shekaru kimanin 20 ke nan da suka wuce.

A shekarar 1997, ma'aikatar kula da ilmi ta Sin ta tura Liu Gaoqiong zuwa kasashen Afrika, sai ya tashi daga jami'ar kula da aikin gona ta Nanjing, don ya ziyarci jami'ar Egerton da ke birnin Nakuru na kasar Kenya, don ba da tallafi game da fasahohin aikin gona a jami'ar. Isar sa ke da wuya sai ya fara kaunar nahiyar Afrika, inda ya tsaida anniyar zama a nahiyar don taimakawa aikin gona a can.

Tumatir ya zama daya daga cikin muhimman kayan lambu na kasar Kenya, shi ne abinci na jama'ar kasar Kenya. A karshen karnin da ya wuce, yawan tumatir da manoman Kenya suka samu bai wuce kan fili na eka 1 kilo 350 ba. Ban da haka kuma, duk lokacin damina, ana fuskantar matsalar kwari, kuma lamarin ya yi illa ga yawan tumatir da aka samu gami da ingancinsu.

Bayan da Liu Gaoqiong ya isa jami'ar Egerton, sai ya gabatar da shawarar kafa dakin dumi don shuke-shuken tumatir, abun da zai iya kau da kwari, kuma zai daukaka ingancin tumatir.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China