in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU za ta bullo da dabarun yakar ta'addanci
2016-02-01 09:36:47 cri

Wani kusa a kungiyar hada kan kasashen Afrika AU ya ce, kungiyar za ta hada gwiwa da kasashen duniya domin ninka kokarinta wajen yaki da ayyukan ta'addanci.

Smail Chergui, shi ne kwamishinan AU na sashen zaman lafiya da tsaro, ya fada a yayin taron manema labaru a lokacin taron karawa juna sani na shugabannin kasashe mambobin kungiyar a Addis Ababa cewar, shugabancin kungiyar zai mai da hankali matuka wajen samar da isassun kayayyakin aiki domin samar da zaman lafiya ta hanyar kakkabe ayyukan ta'addanci.

Kwamishinan ya kara da cewar, za su ninka kokarin da suke wajen lalibo hanyoyin da za su samar da dawwamamman zaman lafiya a yankunan dake fama da tashe tashen hankula, kamar kasashen Sudan ta kudu, da Burundi da yankin babban tafki, ya ce, wannan shi ne muhimmin aikin da za su aiwatar a wannan shekara.

Kwamitin na zaman lafiya da tsaro na AU mai mambobi 15, ya amince da wannan kuduri yayin taron da ya gudanar a Juma'ar da ta gabata, inda ya sha alwashin yaki da ta'addanci a nahiyar Afrika.

Chergui ya ce, shugabannin kasashen mambobin kungiyar sun cimma matsaya wajen hada kai da yin aiki tare don gudanar da ayyukan da za su samar da zaman lafiya da kuma yaki da masu tsattsauran ra'ayi a fadin nahiyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China