in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dala miliyan 282 ake bukata don aikin jin kai a Kamaru a 2016
2016-01-27 10:03:31 cri

MDD ta fada a Litinin nan cewar, a kalla ana bukatar zunzurutun kudi da ya kai dalar Amurka miliyan 282 a wannan shekarar ta 2016 domin amfani da su ga ayyukan jin kai ga mutanen dake cikin kuncin rayuwa a sanadiyyar hare haren mayakan Boko Haram a arewacin jamhuriyar Kamaru, da kuma kwararar mayakan tada kayar baya daga jamhuriyar Afrika ta Tsakiya CAR.

Ko'odinetan MDD Najat Rochdi, ya fada cewa, tun a shekarar 2013 ne, gwamnatin Kamaru da masu tallafa mata, suka kafa gidauniyar neman agaji domin ayyukan jin kai ga mutanen da rikice rikicen suka shafa.

Mutanen da ake sa ran tallafa musu sun hada da wadanda rikicin ya tilastawa barin gidajen su, da 'yan gudun hijira, da sauran al'ummomin kasar wadanda matsalolin yunwa da karancin abinci mai gina jiki, da cutuka suka addabe su.

Jami'in MDD ya ce, a shekarar 2015, duka duka dala miliyan 163 ne aka samu daga cikin dala miliyan 264 da aka bukata.

A cikin kasafin kudin na wannan shekara, ana bukatar dala miliyan 176 ga 'yan gudun hijirar jamhiuriyar Afrika ta Tsakiya, wadanda aka kiyasta yawansu dubu 250 da kuma wasu dubu 70 daga Najeriya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China