Wata daliba mai shekaru 22 ta harbu da cutar a Bamoi, Lumor wani garin kasuwanci dake kan iyaka da kasar Guinea a gundumar Kambia kuma an kai ta garin Magburaka dake gundumar Tonkolli don neman magani inda daga bisani ta rasu inji Abdullai Baraytay, Kakakin ma'aikatar.
Mr. Baraytay yace gwajin da aka yi mata kafin mutuwar ta ya tabbatar da cewa Ebola ne ta kamu da shi.
Hukumar kiwon lafiya daga nan sai ta tunatar da jama'ar kasar cewa ba dama ana nufin ba za'a iya samun sake bullar cutar ba ne don haka mutane su cigaba da kula da dokokin kiwon lafiyar su.