WHO ta ce bayan shafe kwanaki 42 ba a samu wanda ya harbu da Ebola a Liberia ba, wadda ita ce kasa ta karshe da cutar ke yaduwa, ta tabbata cewa an samu nasarar dakile yaduwar ta.
Wannan ne dai karon farko da dukkanin kasashen da cutar ta fi yiwa illa wato Guinea da Laberiya da Saliyo suka kubuta daga cutar, tun bayan barkewar ta shekaru biyun da suka gabata.
A cewar hukumar ta WHO, yaduwar Ebola a wannan karo wanda shi ne mafi tsanani a tarihin cutar, ya hallaka mutane sama da 11,300, cikin jimillar mutane sama da 28,500 da suka harbu.
Duk kuma da irin nasarar da aka cimma a wannan karo, WHOn ta ce dole ne a ci gaba da sanya ido, tare da daukar muhimman matakan kandagarki, musamman ma cikin watanni masu zuwa domin hana sake bullar cutar.