Wannan kira na kunshe ne cikin wata sanarwa da MDD ta rabarwa manema labarai, bayan da aka sanar da kawo karshen cutar a kasar Liberia.
Sanarwar ta ce yanzu haka kasar ta Liberia tana karkashin shirin sa-ido na watanni uku, tun bayan da aka ayyana kawar da cutar a kasashen Guinea da Saliyon, a watanni Nuwamba da Disamban shekarar da ta gabata.
Asusun na UNICEF ya jaddada muhimmancin samarwa wadannan yara da suka shiga halin kunci a kasashe uku da cutar da ta fi addaba sutura, abinci, a kuma sanya su a makaranta.
Don haka, asusun na UNICEF ya yi kira ga al'ummomin kasashen Guinea, Liberia da Saliyo da su ci gaba da taimakawa wadannan yara, ta yadda za su farfado daga mummunan tasirin illar cutar ta Ebola.(Ibrahim)