Sharhin ya bayyana cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da kasashen Larabawa. Don haka, gwamnatin kasar Sin a karon farko ta gabatar da takardar manufofin game da kasashen Larabawa, wadda ke da muhimmanci matuka
Sharhin ya kuma yi kira da a yi amfani da shirin nan na "ziri daya da hanya daya" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, da yin hadin gwiwa da raya dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Larabawa, ta yadda za a samar da sabbin damammaki ga hadin gwiwar da ake yi tsakanin sassan biyu. (Zainab)